Majalisar Ƙoli ta Shari’ar Musulunci a Najeriya (SCSN) ta bayyana rashin jin dadinta kan irin makudan kuɗaɗen da ake batarwa da sunan dakile matsalar tsaro da kuma bunkasa wutar lantarki a kasar ba tare da wani sakamako na azo-a-gani ba.
A bayan nan ne Ministan Tsaro, Alhaji Badaru Abubakar ya tabbatar da cewa, Gwamnatin Tarayya karkashin jagorancin Bola Ahmed Tinubu, tana kokarin yin amfani da fasahar zamani wurin yakar matsalolin tsaro da ke addabar kasar nan musamman ta’addanci.
Sai dai a cikin jawabin da Shugaban Majalisar Ƙolin, Sheikh Abdurrasheed Hadiytullah ya yi yayin buɗe taron wa’azin maraba da watan Azumin Ramadan da aka saba yi shekara-shekara a Kaduna, ya yi kira ga al’ummar Musulmi da su jajirce wajen ganin gwamnatin tarayya ta kawo karshen cin hanci da rashawa, da almubazzarancin da ake yi da dukiyar al’umma.
Sheikh Hadiytullah ya koka kan yadda talakawan Najeriya ke ɗaukar nauyi da goyon bayan almubazzaranci da shugabanni ke yi.
- Peter Obi Ya Dauki Nauyin Bakanon Da Ya Mayar Da Tsintuwar N15m
- Jeff Bezos ya karɓe ragamar mai kuɗin duniya daga hannun Elon Musk
Ya buƙaci shugabanni da su samo sabbin dabarun siyasa, da hanyoyin magance matsalar cin hanci da rashawa domin tabbatar da zaman lafiya a kasar.
Shugaban majalisar koli ta Shari’a ya umarci al’umma da su nisanci kalaman tada husuma, yayin wa’azi a ciki da wajen watan azumin Ramadan.
Haka zalika ya kara da cewa, Musulunci ba addinin tashin hankali ba ne, addinin soyayya da hadin kai ne.
Ya ce, “Ya kamata mu ci gaba da yin kira ga gwamnatoci da su ɗauki kwararan matakai don magance matsalar cin hanci da rashawa, cin amanar kasa da almubazzaranci.
“Saboda cin hanci da rashawa tamkar ciwon daji ne, wanda ke ruguza duk wani abu mai daraja da kuma bata ka’idojin shugabanci na gari.”
Ya ce, daidai ne mu tambayi shugabanninmu, mene ne zai sa talakan Najeriya ya ɗauki nauyin rashin tsaron da ake kashe tiriliyoyin daloli a fannin tsaro ba tare da wani sakamakon a-zo-a-gani ba?
“Mene ne ya sa talakan Najeriya zai riƙa fuskantar matsalar wutar lantarki da tsadarta, duk da irin biliyoyin dalolin da ake narkarwa a kan lantarki?
“Ko shakka babu, ba za mu sa rai cewa za mu samu mafita dangane da al’amuran da ke dagula rayuwarmu ba har sai shugabanninmu sun sa ido akan ‘yan siyasa, don magance matsalar cin hanci da rashawa a kowane lokaci, a ko’ina da kuma duk wanda ke da hannu a ciki.
“Muna kira ga gwamnatin tarayya da ta sake nazarin tsarin tattalin arzikin kasar nan, domin kuwa tsarin ya jefa yan kasar nan a cikin mawuyacin hali.”
Yayin da watan Ramadan ke gabatowa, ya yi kira ga al’ummar Musulmi da su himmatu wajen yin addu’o’in samun zaman lafiya a Nijeriya.
Ya yi kira ga masu ruwa da tsaki da suka haɗa da gwamnati da kungiyoyin farar hula da kuma kamfanoni masu zaman kansu da su hada kai yadda ya kamata wurin magance matsalolin rashin tsaro da aiwatar da ingantattun dabarun kawar da shi.