✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Majalisar Zartaswa ta amince ta karin Naira tiriliyan 2.1 a Kasafin Kudin 2023

Za a ware wa Abuja Naira biliyan 100, domin aiwatar da wasu ayyukan raya birnin cikin gaggawa.

Majalisar Zartaswa ta Ƙasa (FEC), ta amince ta karin Naira N2,176,791,286,033 a Kasafin Kudin 2023.

Ministan Kasafi da Tsare-tsaren Tattalin Arziki, Atiku Bagudu ne ya bayyana haka ga manema labarai a Fadar Shugaban Ƙasa, bayan kammala taron Majalisar Zartaswa wanda Shugaban Kasa Bola Tinubu ya ya jagoranta wannan Litinin din a Abuja.

A cewar Bagudu, abubuwan da kasafin zai fi maida hankali a kai su ne batun inganta tsaro sai kuma biyan albashin ma’aikata da alawus-alawus na haƙƙoƙin su.

“A yau Majalisar Zartaswa ta amince ta nemi Naira tiriliyan 2, 176, 791,286.33, waɗanda kuɗaɗe ne domin kashe su wajen wasu muhimman batutuwa na gaggawa a cikin 2023.

“Daga cikin kuɗaɗen akwai Nairai biliyan 605 waɗanda za a kashe wajen tsaron ƙasa, domin samun ɗorawar nasarar da aka samu baya-bayan nan a fannin tsaro. Kuɗaɗe ne da ɓangarorin sojojin ƙasar nan da sauran fannonin tsaron ƙasar nan ke buƙata a cikin 2023.

“Haka kuma akwai Naira biliyan 300 domin gyara gadoji, ciki kuwa har da gadar Eko da ta ‘Third Mainland’ sai kuma ginin wasu titina, gyaran wasu da kuma aikin kula da wasu titinan da dama, kafin sake dawowar ruwan sama.

“Akwai Naira biliyan 200, domin inganta harkokin noma ta hanyar sayo kayan gona, domin bunƙasa noma da wadatar abinci a ƙasa.

“Sai kuma Naira biliyan 200 da za a kashe ta hanyar biyan albashi da sauran haƙƙoƙin ma’aikata.”

Ya tunatar da ƙarin Naira 35,000 na albashin ma’aikata su kimanin miliyan 1.5, wanda za a fara biya tun daga watan Satumba, Oktoba, Nuwamba da Disamba, duk su na cikin kasafin na ƙarshen shekarar 2023.

Bagudu ya ce za a ware wa Babban Birnin Tarayya Abuja Naira biliyan 100, domin aiwatar da wasu ayyukan raya Abuja da kewaye cikin gaggawa.

Sannan kuma akwai Naira biliyan 5.5 da za a kashe wajen bai wa ɗalibai lamunin karatu. Sai kuma sabbin Ma’aikatun Sabbin Ministoci za a kashe masu naira biliyan 8 domin su fara aiki gadan-gadan.

“Bagudu ya ce za a kashe Naira biliyan 18 wajen shirya zaɓen gwamnonin Kogi da Bayelsa, a ranar 11 ga Nuwamba, 2023.

Bagudu ya ce a cikin kasafin kuma akwai Naira biliyan 400, wadda Gwamnatin Tarayya ta ɗora kan bashin Dala miliyan 800 da za’a raba wa marasa galihu Naira 25,000 ga gidaje miliyan 15 a faɗin ƙasar nan.