✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kasafin 2024 zai kai watan Yunin 2025 – Akpabio

Tinubu ya gabatar da kasafin kuɗin shekarar 2025 a gaban majalisar dokokin.

Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya bayyana cewa wa’adin kasafin kuɗin shekarar 2024 kai har zuwa ranar 25 ga watan Yuni, 2025.

Ya bayyana haka ne a ranar Laraba, yayin da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya gabatar da kasafin kuɗin shekarar 2025 a zauren Majalisar Dokokin Ƙasa.

Akpabio, ya bayyana cewa kasafin 2024 ya samu nasarar kashi 50 na ayyukan manyan gine-gine da kuma kashi 48 na kuɗin tafiyar da gwamnati.

Shugaba Tinubu, ya gabatar da kasafin kuɗi na Naira tiriliyan 47.9 na shekarar 2025 domin tantancewa da yin nazari.