✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zulum ya gabatar da N584.76bn a matsayin kasafin kuɗin 2025

Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya gabatar da kasafin kuɗin shekarar 2025 na Naira biliyan 584.76. 

Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya gabatar da kasafin kuɗin shekarar 2025 na Naira biliyan 584.76.

Kasafin zai mayar da hankali ne kan ɓangaren lafiya, ilimi, da farfaɗo da tattalin arziƙi, tsaro, samar da ababen more rayuwa, da ayyukan jin-ƙai.

Kakakin gwamnan, Kwamared Dauda Iliya, ya bayyana cewa za a yi amfani da kuɗaɗen ne daga asusun da gwamnati ke samu daga FAAC, harajin cikin gida (IGR), da tallafi daga ƙungiyoyin daban-daban.

A ɓangaren lafiya, an ware Naira biliyan 89.97, wanda ya kai kashi 15.39 na kasafin kudin.

Gwamna Zulum, ya ce za a gina asibitin ƙashi a Maiduguri, tare da sabbin manyan asibitoci a Magumeri, Gubio, Azare, Uba, Dikwa, Kaleri, da Mafa.

Hakazalika, za a gyara asibitocin Baga da Mulai, sannan a kammala asibitin koyarwa na Jami’ar Jihar Borno.

Har ila yau, za a faɗaɗa tsarin inshorar lafiyar ma’aikatan gwamnati da marasa galihu a dukkanin ƙananan hukumomi 27 da ke jihar.

A ɓangaren ilimi, an ware Naira biliyan 69.81 domin samar da sabuwar makarantar zamani (chance) ta biyu, tare da gina ƙarin makarantun Mega guda biyar da manyan makarantun Islamiyya guda biyar.

Haka kuma, za a gyara makarantu 50 a faɗin jihar tare da samar musu da kayan aiki.

Gwamnan ya bayyana cewa an tanadi isassun kuɗaɗe domin tallafa wa matasa, samar da ayyukan yi, da kuma inganta rayuwar al’ummar Jihar Borno baki ɗaya.

Wannan kasafin kuɗin, a cewarsa, zai ƙara bunƙasa ci gaban jihar da kuma inganta rayuwar jama’a.