A yayin zamanta na ranar Alhamis, Majalisar Wakilai ta karrama hazikin dan sanda, DCP Abba Kyari bisa bajintar da yake nunawa a aikinsa.
Karrama Kyari, wanda shi ne Shugaban Rundunar Tattara Bayanai da Kawo Dauki da Babban Sufeton ‘Yan Sanda ya kafa, ta biyo bayan kudirin da dan majalisa Ahmed Jaha daga jihar Borno ya gabatar na bukatar yin hakan ranar Talata.
A cewar dan majalisar, Kyarin ya cancanci karramawar saboda namijin kokarinsa wajen yaki da rikakkun masu laifi a Najeriya.
Jaha ya bayyana shi a matsayin hazikin matashin dan sanda da ya tsere sa’a tsakanin takwarorinsa ta bangaren aikinsa wanda kuma ya yi aiki a bangarorin kasa da dama.
Irin nasarorin da Kyarin ya samu dai sun hada da kama rikakkun mai garkuwa da mutanen nan da aka fi sani da Evans da kuma White Vampire.
Ya kuma kamo wadanda suka hallaka tsohon Babban Hafsan Tsaro na kasa Alex Badeh, sannan ya kama wasu daga cikin manyan kwamandojin kungiyar Boko Haram da masu kera musu bama-bamai da dai sauransu.
Da yake jawabi yayin karramawar, Kakakin Majalisar Femi Gbajabiamila ya ce sun yanke shawarar karrama dan sandan ne sakamakon irin yadda ya yi zarra a aikinsa tsakanin takawarorinsa.
A cewar Ggajabiamila, hakan ya yi dai dai da kudurin majalisar na tara na ganowa tare da zakulo hazikan ma’aikata a kowanne fanni na rayuwa da nufin yaba wa kokarinsu don kara karfafa musu gwiwa da kara musu kaimi.