Majalisar Wakilai za ta yi zaman gaggawa a ranar Laraba domin gyara wani kuskure da aka samu a cikin Dokar Zabe ta 2022.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Magatakardan Majalisar, Dokta Yahaya Dan Zaria ya fitar a ranar Talata.
- Ban kai ga yanke shawara kan sauya sheka ba — Shekarau
- Barau ya fasa takarar Gwamnan Kano, zai fafata da Ganduje a kujerar Sanata
Wannan na zuwa ne yayin da Majalisar Dattawa ta yi wa Dokar Zaben kwaskwarima yayin zamanta na ranar Talata.
A cewar Magatakardan, “Wannan na sanar da daukacin ‘yan uwa da ma’aikata da kafafen yada labarai da sauran jama’a cewa majalisa za ta yi zaman gaggawa a gobe Laraba 11 ga Mayu, 2022 da misalin karfe 11:00 na safe.
“Wannan zama ne na musamman da ya zama wajibi domin gyara wani kuskure a cikin Dokar Zabe.
“Majalisa ta yi nadamar wannan gajeriyar sanarwar tare da yin kira ga dukkan ‘yan majalisar da su halarta”.
An yi wa dokar gyaran fuska ne domin bai wa wakilan da suka kafa doka damar kada kuri’a a zaben fidda-gwani na jam’iyya, wadda Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sanya wa hannu.