Bayan cece-kuce da ba hammata iska, daga karshe dai Majalisar Wakilai a ranar Juma’a ta amince da Kudurin Dokar Zabe ta Kasa da kuma Kudurin Dokar Man Fetur (PIB).
An dai amince da kudurorin ne bayan yi musu karatun dalla-dalla a zauren majalisar.
Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar, Alhassan Ado Doguwa ne dai ya gabatar da bukatar amincewa da kudurorin, yayin da mataimakinsa, Peter Akpatason ya goyi bayan bukatar.
Mataimakin Kakakin Majalisar, Ahmed Idris Wase ne dai ya jagoranci zaman majalisar.
Tun da farko dai sai da mambobin jam’iyyar adawa ta PDP a zauren Majalisar suka fice daga zauren saboda nuna rashin amincewarsu da wasu sadarorin dokokin masu cike da cece-kuce.
Shugaban Marasa Rinjaye a zauren, Ndudi Elumelu ne ya jagoranci sauran takwarorinsa wajen ficewar bayan sun jawo hankali kan yunkurin amincewa da wasu sadarorin kudurorin, duk da cewa ba a cimma matsaya a kan su ba.
Ya ce ba zai yuwu ’yan adawar su zauna su zuba ido ana yin karan tsaye ga bukatunsu a majalisar ba.
Majalisar ta kuma amince da a rika amfani da intanet da kuma takardu wajen aikewa da sakamakon zabe a inda daya daga cikin biyun zai fi zama maslaha.