Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya sanar da kafa wani kwamitin kar-ta-kwana da zai yaki matsalar kwacen waya da ta addabi Jihar a ‘yan kwanakin nan.
Ya sanar da hakan ne a cikin jawabin da ya gabatar bayan an rantsar da shi a filin wasa na Sani Abacha da ke Kano, da safiyar Litinin.
- Zan karbo duk kadarorin gwamnati da Ganduje ya sayar ba bisa ka’ida ba – Abba
- Ba zan yi mulkin kama-karya ba – Tinubu
Ya alakanta matsalar da yawan shaye-shayen kwayoyi, wadanda ya ce su suke rura wutar kowanne aiki assha.
Sabon Gwamnan ya ce, “A yau, ina sanar da kafa wani kwamitin kar-ta-kwana da zai rika yaki da masu kwacen waya da sauran laifuffuka.
“Kwamitin zai kunshi jami’an tsaro daban-daban da kuma kotunan taf-da-gidanka, wadanda za su rika rika aiki tare wajen kawo karshen wadannan batagarin daga tituna da unguwanninmu.
“Kazalika, za mu sake bude makarantar horar da kangararrun yara ta garin Kiru, nan ba da jimawa ba, saboda ta ci gaba da gyaran halin ‘yan kwaya,” in ji Abba.
Aminiya ta raiwato cewa ana kammala rantsuwa, ko kafin ya tafi gidan gwamnati sai da Abba ya ziyarci makarantar a garin na Kiru domin farkar da ma’aikanta cewa za ta dawo aiki gadan-gadan.