Babbar Kotun Tarayya da ke Jihar Kano ta dakatar da daukar mataki kan Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Wakilai, Alhassan Ado Doguwa.
Kotun da mai shari’a Mohammad Yunusa, ya jagoranta a ranar Litinin, ta ce tana da hurumin saurare tare da bayar da belin wanda ake tuhuma kan Naira miliyan 500.
- Matatar Dangote za ta samar da dunbin ayyuka ga matasa –Dangote
- Buhari da Shugabannin kasashen Afirka 5 na halartar kaddamar da matatar man Dangote
Ta kuma bayyana cewa laifin kisan kai da wasu tuhume-tuhume da ake zargin Doguwa da ke gaban babban alkalin Kano ya saba wa kundin tsarin mulki.
Da yake yanke hukunci a kan bukatar da Doguwa ya gabatar na tabbatar da hakkinsa na dan Adam, Mai shari’a Yunusa, ya ce babban kotun majistare ba ta da hurumin yanke hukunci kan shari’ar da ake yi wa Doguwa.
Mai shari’a Yunusa ya kuma bayar da misali da sashe na 251 (1) wanda ya bai wa Babbar Kotun Tarayya damar sauraren kara kan makami kamar yadda ke kunshe cikin tuhumar da ake yi wa Doguwa.
Alkalin kotun, ya kara da cewa bayar da belin Doguwa ba yana nufin hana sauraren shari’a ba ne, amma dole ne a bi tsarin da ya dace.
Lauyan Doguwa, Nureini Jimoh (SAN) ya bayar da hujjar cewa ’yan sanda sun tsare Doguwa ba bisa ka’ida ba, kuma suna adawa da ’yancinsa kamar yadda yake a kundin tsarin mulkin 1999 da aka yi wa kwaskwarima.
Da yake nuna rashin gamsuwarsa kan belin Doguwa, dan sanda mai shigar da kara, AB Saleh, ya ya ce matakin da Mai shari’a Yunusa ya dauka ya zama babban cin zarafi ga tsarin kotun.
Amma da yake yanke hukunci a ranar Litinin, Mai shari’a Yunusa ya ce tun da farko bai kamata a tasa keyar Doguwa zuwa gidan gyaran hali ba saboda ba a gurfanar da shi a gaban kotu ba.
Kuma ba a bincike shi yadda ya kamata ba, ya ce bai kamata ’yan sanda su gurfanar da shi a gaban karamar kotu ba, wanda hakan ya saba da kudin tsarin mulki.