Majalisar Tattalin Arziki ta Ƙasa a Najeriya ta ba da shawarar dakatar da ƙudirin yi wa haraji kwaskwarima da gwamnatin tarayya ke shirin yi.
Mambobin majalisar National Economic Council (NEC) sun ƙunshi gwamnoni ƙarƙashin jagorancin Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima.
- Ruftawar gini ta laƙume rayukan mutum 10 a Ibadan
- An ƙara mafi karancin albashin Kaduna zuwa N72,000
Da yake magana da manema labarai bayan zaman majalisar a yau Alhamis, Gwamnan Oyo Seyi Makinde ya ce sun yanke shawarar dakatar da ƙudirin ne bayan cece-kucen da ya biyo baya “da zummar bai wa masu ruwa da tsaki dama.
Bayan kammala taron da ta gudanar a ranar Lahadi, Ƙungiyar Gwamnonin Arewa (NGF) wadda Gwamnan Gombe Inuwa Yahaya ke jagoranta, ta ƙi amincewa da shirin ƙara harajin VAT.
Daga bisani shi ma Gwamna Abdullahi Sule na Jihar Nasawara, ya kare matakin da cewa sabon tsarin ƙara harajin zai zamo wata babbar illa ga Arewacin ƙasar.
A yau Alhamis ne Fadar Shugaban Ƙasa ta ce ta aike wa Majalisar Dokoki ƙudirin gyaran karɓar harajin domin amincewa da shi.