✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kungiyoyin addini na shirin dakile COVID-19 a wuraren ibada

Manyan addinai a Najeriya na tsara matakansu na dakile yaduwar kwayar cutar coronavirus a masallatai da coci-coci idan gwamnati ta sake bude su a kasar.…

Manyan addinai a Najeriya na tsara matakansu na dakile yaduwar kwayar cutar coronavirus a masallatai da coci-coci idan gwamnati ta sake bude su a kasar.

Majalisar Koli ta Addinin Musulunci (NSCIA) da Kungiyar Kiristocin ta Najeriya (CAN), kowaccensu ta dauki matakin ne bisa shawarar shugaban Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa (NCDC) Chikwe Ihekweazu.

Majalisar Musuluncin ta kafa kwamitin da zai tsara matakan da masallatai za su bi bayan bude su ta yadda cutar ba za ta yadu ba.

Sakataren Majalisar Ibrahim Aselemi ya ce nan gaba za a sanar da tsare-tsaren da kwamitin ya yi wa masallatai.

A nata barayin, CAN na tattaunawa da bangarorinta don cimma matsaya kan matakan da coci-coci za su bi na hana yaduwar cutar.

Mai Magana da Yawun shugaban kungiyar Adebayo Oladeji, ya ce shugabannin kungiyar na kan tattauna lamarin. Adebayo ya ce matakan da CAN za su fi karkata ne kan bayar da tazara da tsaftace hannu.

Kungiyar na kokarin kammala aiki domin mika tsare-tsarensu ga NCDC a kan kari.

A yau Laraba shugaban CAN Reverend Supo Ayokunle ke ganawa da jagororin kungiyar domin yin shawara game da matakan da za su dauka.

Matakana da bangarorin addinan ke dauka na zuwa ne bayan shugaban NCDC Chikwe Ihekweazu ya shawarci kungiyoyin kwararru da na addinai da wuraren ibada su gabatar da tsare-tsare da suke son bi domin hana cutar COVID-19 yaduwa yayin gudanar da harkokinsu.

Ikeazu ya ce tuni kungiyar masu sufuri tsakanin jihohi suka mika wa NCDC matakan da suka tsara domin  neman a bude harkokinsu.

Ya ce NCDC za ta yi nazari sannan ta ba kungiyar shawarwari, sannan ya bukaci sauran kungiyoyi da bangarori su bi sahu.

Ya bayyan haka ne a ranar Alhamis a lokacin taron kwatin fadar shugaba kasa na yaki da COVID-19.