Majalisar Hadin Gwiwa Tsakanin Musulmai a Jihar Sakkwato ta yi wa Babban Bishop na Cocin Katolika a Jihar, Rabaran Mathew Hassan Kukah kashedi kan kalamansa na cin zarafin Musulunci da Musulman Arewacin Nijeriya.
Majalisar wadda mahada ce ta kungiyoyi, cibiyoyi da darikun Musulunci da limamai da masu da’awa a Jihar Sakkwato ta yi tir da sakon Rabaran Kukah na Kirsimeti inda a ciki ya soki Musulunci da Musulmai.
- Ganduje zai ba Kwankwaso sarautar mahaifinsa
- Saki a fim: Yadda fatawar Dokta Bashir ta tayar da kura
- Kotu ta yanke wa soja hukuncin kisa ta haryar harbi
A sakon na Rabaran Kukah, ya yi zargin cewa da wani Musulmi wanda ba dan Arewa ne ya aikata abubuwan da Shugaba Buhari ya yi na nuna fifiko da tuni an yi masa juyin mulki a kasar nan.
Don haka Majalisar ta bayyana damuwarta cewa akwai wata makarkashiya a cikin kalaman na Bishop Kukah.
Mukaddashin Shugaban Majalisar, Farfesa Isa Muhammad Maishanu y shaida wa manema labarai cewa manufar su ita ce kare kimar Musulunci da Musulmai da Mista Kukah ke jin dadin suka koyaushe ba tare da jin nauyin magana irin haka ba; amma su ba kare Buhari suke yi ba.
“Tun asali Bishop nada sha’awar yin magangannu masu kawo rudani ya tsokani Musulmi, har yana bugun kirjin wai kashe-kashen da ake yi a Najeriya wani bangare ne na addini ya shirya!
“Masu hankali sun san gaskiya, mun yi mamakin yadda Rabaran Kukah ke zaune lafiya cikin jin dadi a cibiyar Daular Usmaniya amma yake irin wannan magana da hankali ba zai dauka ba.
“Kyamar da yake wa Musulmai ta makantar da shi duk da yana kurarin cewa yana addinin soyayya,” a cewar Farfesa Maishanu.
Ya ce ba karon farko ba ke nan, Bishop Kukah kan yi hakan lokaci-lokaci musamman idan ya tara ’yan jarida da yake zaba saboda alakarsa da su, ko kuma a hudubobinsa inda yake yin mummunar suka ga Musulmai ’yan Arewa.