Majalisar Dokokin Jihar Kano karkashin jagorancin shugabanta Honorabul Abdul’aziz Garba Gaffasa, ta umarci kwamitinta da ke kula da korafe korafen jama’a da ya binciki zargin da ake yi wa Mai martaba Sarkin Kano Sunusi Lamido Sunusi II akan wasu halaye da ya suka ci karo da al’adu da mutuncin al’ummar Jihar Kano.
Majalisar ta bayar da wannan umarnin ne biyo bayan kudurin da dan majalisar kuma Shugaban Kwamitin da ke kula da kananan Hukumomi a majalisar Honorabul Alhaji Zubairu Hamza Masu.
Dan majalisa Zubairu Hamza Masu, ya shaida wa majalisar cewa, kwamitinsa ya karbi korafin ne daga wata kungiya da ke faffutuka wajen ci gaban ilimi da al’adu karkashin shugabancin Muhamamd Bello Abdullahi da kuma Muhamamd Mukhtar Jaen, inda suka zargi Sarkin da cewa yana nuna halayen da suke zubar da kimar al’ummar Jihar Kano.
Ganduje ya bude wani sabon bincike kan Sarkin Kano
Ganduje ya gindaya sharudda akan sulhunsu da Sarkin Kano