✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Majalisar Kano ta amince da karin N55bn a kasafin kudin 2022 

Majalisar ta dage zamanta har zuwa ranar 19 ga watan Disamba.

Majalisar Dokokin Jihar Kano, ta amince da karin naira biliyan 55 a kasafin kudin jihar na bana.

Amincewar ta zo ne bayan karatu na uku da aka yi wa kudirin jim kadan bayan amincewa da rahoton da shugaban Kwamitin Kasafin Kudi na majalisar, Alhaji Abba Ibrahim, ya gabatar yayin zaman da shugaban majalisar, Alhaji Hamisu Chidari ya jagoranta.

Ibrahim ya ce an yanzu an kara Kasafin Kudin na bana zuwa sama da Naira biliyan 276,  bayan bukatar Gwamna Abdullahi Ganduje ya gabatar na bunkasa ci gaban jihar.

Dan majalisar ya bayyana cewa, an kara karin kasafin kudin daga Naira biliyan 43 zuwa naira biliyan 55 domin gudanar da ayyukan Hukumar Kula da Ilimin Bai Daya ta jihar (SUBEB) da sauran ayyuka.

A cewarsa, tare da amincewa da karin Kasafin Kudin, abin da ake kashewa manyan ayyuka a yanzu ya kai Naira biliyan 160, yayin da abin da ake kashewa na yau da gobe ya kai Naira biliyan 115.

Kamfanin Dillancin Labarai (NAN), ya ruwaito cewa majalisar ta dage zamanta zuwa ranar 19 ga watan Disamba domin ba da damar kare kudurin kasafin kudin.