Majalisar dokokin jihar Kano a yau Laraba ta amince da sunayen sababbin Kwamishinoni 4 da Gwamnan Jihar Abdullahi Ganduje ya tura wa zauren majalisar.
Kakakin majalisar dokokin jihar Alhaji Kabiru Rurum ya ce, majalisar ta karbi wasikar da Gwamna Ganduje ya aikawa majalisar a ranar 27 ga Disamba 2018 don tantance sunayen da amincewar zauren majalisar.
‘Yan majalisar sun amince da sunayen sababbin Kwamishinonin bayan kwamitin tantancewa ya mika rahotansa.
Kwamishinonin sun hada da: Malam Bashir Yahaya-Karaye da Alhaji Mukhtar Ishak-Yakasai da Alhaji Shehu Kura da kuma Alhaji Muhammad Tahir wanda aka fi sani da Baba Impossible.