Majalisar Dokokin Jihar Kuros Riba ta tsige kakakinta, Honarabul Elvert Ekom Ayambem a wannan Larabar.
Honarabul Effiong Ekarika mai wakiltar Calabar ta Kudu 1 ne ya gabatar da ƙudirin tsige kakakin yayin da Omang Omang mai wakiltar Ƙaramar Hukumar Bekwara ya goyi bayansa.
- Asibitin Benin zai binne gawarwaki 270 da aka rasa ’yan uwansu
- Bakin Kwari Masu Wari Na Barazana ga Mazaunan Ondo
Bayanai sun ce mambobin majalisar 17 daga cikin 25 ne suka amince da tsige kakakin nata sakamakon zarginsa da ɓarnatar da kuɗi, rashin kiyaye dokokin majalisar da sauransu.
Tun a ranar Talata ce ’yan majalisar suka fara yunƙurin tsige kakakin, inda kusan ’yan majalisar 20 suka goyi bayan ƙudirin tsige ɗan majalisar mai wakiltar Ƙaramar Hukumar Ikom 2.
’Yan majalisar sun kuma zargi kakakin da yin ruf da ciki kan Naira miliyan 48 da biyan kuɗin wutar lantarki da kuma sama da Naira miliyan 404 da Hukumar Tattara Haraji ta ware domin ƙarasa ayyukan da aka samu giɓi.
A watan Yunin 2023 ne aka zaɓi Honarabul Elvert Ayambem a matsayin kakakin majalisar dokokin jihar ta 10.