Majalisar Dokokin Jihar Kuros Riba, ta dakatar da shugabar Ƙaramar Hukumar Bekwara, Hon. Theresa Ushie, na tsawon wata uku, domin a gudanar da bincike kan wasu zarge-zarge da ake mata.
An ce kimanin wakilan ƙaramar hukumar 10 daga cikin 11 ne suka yi ƙarar shugabar, inda tara daga cikinsu suka rattaba hannu suna goyon bayan a dakatar da ita.
- Gwamnatin Kano za ta binciki musabbabin gobarar kasuwar Farm Center
- Za a dauke wa jihohin Arewa maso Gabas wutar lantarki na tsawon kwana 4
Ɗaya daga cikin wakilan ne kawai bai yarda ba.
Ana zargin Hon. Ushie da amfani da kuɗin Ƙaramar Hukumar ba tare da shawarar majalisar jihar ba, tare da yin wasu muhimman ayyuka ba tare da tuntuɓar ’yan majalisar ba.
Mai magana da yawun Gwamnan jihar, Nsa Gill, ya bayyana cewa an dakatar da shugabar ne domin a samu damar yin cikakken bincike cikin kwanciyar hankali.
Shugaban majalisar dokokin jihar, Rt. Hon. Elvert Ayambem, ya ce an ɗauki wannan mataki ne bisa sashe na 14(3) na dokokin ƙananan hukumomin jihar da aka kafa tun 2005.
A halin yanzu, majalisar ta amince da naɗa mataimakin shugaban ƙaramar hukumar, Hon. Egbung Odama, a matsayin shugaban riƙo har zuwa lokacin da binciken zai kammala cikin wata uku masu zuwa.