✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Majalisar dokokin Kano ta yi watsi da dokar gyaran haraji

Majalisar ta ce ba ta amince da ƙudirin gyaran dokar ba saboda yankin Arewa ne zai faɗa tsaka mai wuya.

Majalisar Dokokin Jihar Kano, ta yi watsi da ƙudirin dokar gyaran haraji da ake tattaunawa a Majalisar Tarayya.

A zaman majalisar na ranar Litinin, ƙarƙashin jagorancin Kakakin Majalisar, Rt. Hon. Isma’il Falgore, ’yan majalisar sun bayyana rashin amincewarsu da ƙudirin bayan muhawara kan illarsa.

Shugaban Masu Rinjaye na majalisar, Hon. Lawan Husseini, mai wakiltar mazaɓar Dala, ya ce dokar za ta cutar da jihohin Arewa idan aka amince da ita.

Ya ce, “Wannan wani shiri ne na lalata tattalin arziƙin yankinmu da ƙara matsin rayuwa.”

Ya ƙara da cewa, “Yadda za a raba harajin na VAT ba adalci ba ne, domin jihohi irin su Legas ne za su amfana sama da kowa, yayin da jihohin Arewa za su ke samun kaso mafi ƙaranci.”

Shi kuwa Hon. Salisu Mohammed, mai wakiltar Doguwa, ya buƙaci Majalisar Dattawa ta mayar da hankali kan matsalolin tsaro da rashin aikin yi maimakon gaggauta amincewa da dokar.

Ya ce, “Dole ne mu fifita magance matsalolin da suka fi damun ‘yan Najeriya.”

Majalisar ta buƙaci ’yan majalisun Arewa da kuma Ƙungiyar Kakakin Majalisu su ɗauki matakin gaggawa don daƙile wannan ƙudiri.

Ta kuma yi gargaɗin cewa muddin aka amince da dokar gyaran haraji, hakan zai ƙara talauci da raunana tattalin arzikin jihohin Arewa.

Idan ba a manta ba Shugaba Tinubu ya aike wa majalisun tarayya ƙudirin gyaran dokar haraji, amma ƙudirin ya bar baya da ƙura.

Mutane da dama da suka haɗar da ’yan siyasa, masana tattalin arziƙi da masu fashin baƙi kan al’amuran yau da kullum sun ce dokar za ta iya durƙusar da Arewa matuƙar aka aminta da ita.

Yanzu haka dai ƙudirin ya haifar da zazzafar muhawara musamman a kafafen sada zumunta da na watsa labarai.