✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Majalisar dokokin Filato ta amince da kasafin kuɗin 2025

Majalisar ta amince da kasafin ne bayan yin nazari da kuma gabatar mata da rahoto.

Majalisar Dokokin Jihar Filato, ta amince da kasafin kuɗin Naira biliyan 529.4 na shekarar 2025.

Kasafin ya haura sama da Naira miliyan 500 daga Naira biliyan 471.134 da Gwamna Caleb Mutfwang ya gabatar da farko.

Majalisar dokokin ta amince da kasafin a zaman da ta yi a ranar Litinin, ƙarƙashin jagorancin shugabanta, Gabriel Dewan.

Majalisar ta amince ne, bayan Hon. Adamu Aliyu, shugaban kwamitin kasafin kuɗi, ya gabatar da rahoto kan kasafin.

A farkon watan Disamban 2024 ne, Gwamna Mutfwang, ya gabatar da kasafin kuɗin wanda ya ƙunshi Naira biliyan 201.5 na kuɗin gudanarwa da Naira biliyan 269.6 na ayyuka.

Bayan tantancewa da nazari, majalisar ta yanke shawarar ƙara kasafin kuɗin zuwa Naira biliyan 529.4.