Majalisar Dattawa ta gayyaci Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN) da ya bayyana a gabanta sakamakon halin da tattalin arzikin kasar ke ciki da kuma faduwar darajar naira a kasuwar kudaden waje.
Majalisar a yau Laraba ta hannun kwamitinta mai kula da harkokin bankuna da inshora da sauran cibiyoyin kudi ce ta gayyaci Mista Olayemi Cardoso.
- ’Yan bindiga sun sace mata biyu ’yan gida daya a Abuja
- Yau Liverpool za ta karbi bakuncin Chelsea a Anfield
Majalisar ta nemi Mista Cardoso da ya bayyana a gabanta ranar Talata mai zuwa domin bayar da bahasi kan matsalolin da ke neman gurgunta tattalin arzikin kasar.
Kwamitin karkashin shugabancin Sanata Adetokunbo Abiru ya gana ne bayan da a yau dala daya ta kai naira 1,520 a kasuwar musayar kudaden waje ta bayan fage, inda suka mika gayyatar ga gwamnan na CBN domin ya je ya yi bayani kan mafita.
A hirarsa da manema labarai bayan taron nasu na sirri, Sanata Abiru ya ce, halin da tattalin arzikin Najeriyar ke ciki musamman hauhawar farashin kayayyaki abu ne da ya damu ‘yan majalisar.