Majalisar Dokokin Amurka, ta bukaci Mataimakin Shugaban Kasar, Mike Pence da Majalisar Ministoci su ba ta damar sauke Shugaba Donald Trump daga mukaminsa idan ya kasa sauke nauyin da ke kansa.
Shugabar Majalisar, Nancy Pelosi ta ce idan bangaren zartarwa ya ki amincewa, Majalisar za ta “fara aikin tsige” Trump saboda tunzura masu zanga-zangar da suka yi tarzoma a ginin Majalisar na Capitol.
- Lambar NIN: Ba za a rufe layukan waya ba
- Ba zan daina fim saboda aure ba —Rahama Sadau
- Facebook da Instagram sun dakatar da shafukan Trump har ya sauka daga mulki
“Ina kiran ne saboda cin mutunci mara misali da Shugaban Kasa ya yi wa kasarmu da al’ummarta,” inji Pelosi, wadda ta ce Trump “mutum ne mai matukar hadari da bai kamata a bari ya ci gaba da mulkin kasar ba.”
Hakan na zuwa ne yayin da Trump ke da kasa da mako biyu ya mika mulki ga wanda ya kayar da shi a zabe, Joe Biden na jam’iyyar Democrat.
Tun da farko, Shugaban Sanatocin Democrat, Charles Schumer ya yi makamancin wannan kira, inda ya ce idan banganre zartarwa ya ki sauke Trump, to Majalisa za ta tsige shi, kuma har sun fara neman goyon bayan hakan.
A ranar Laraba daruruwan magoya bayan Trump suka mamaye ofishin ’yan sanda da ke Capitol, suka farfasa abubuwa, har ta kai kai ga ’yan sanda sun bude wuta da ya yi sanadin mutuwar wata mata.
An shafe awanni ana dauki ba dadi kafin a shawo kan masu boren da ke neman hana Majalisar tabbatar da zaben Biden da kuma ba shi takardar shaidar cin zaben.
Akalla jam’ian ’yan sanda 50 ne suka samu raunuka, yawancinsu na kwance a asibiti sakamakon tarzomar, kuma an cafke sama da mutum 50 daga cikin masu yin ta.
Gabanin zanga-zangar, Trump ya yi wa magoya bayansa jawabi inda ya bukaci su yi maci zuwa Capitol su matsa wa ’yan Majalisar Dattawan Jam’iyyarsa ta Republican da ba sa son a soke sakamakon zaben.
Ya yi hakan ne kasa da mako biyu kafin a rantsar da Joe Biden da Mataimakiyarsa Kamala Harris a matsayin Shugabannin Kasa da Mataimakiyar Shugaban Kasa.
Idan ba ma manta ba, a safiyar Alhamis, zaman hadin gwiwar da Majalisar ta yi a Capitol ya tabbatar da Biden da Kamala a matsayin wadanda suka ci zaben Shugaban Kasar da aka gudanar a watan Nuwamban 2020.