Majalisar ɗinkin duniya ta ce sabon kutsen Isra’ila a yankin Deir Al-Balah na Gaza ya tilasta mata dakatar da ayyukan agajin da take bayarwa.
Hukumar bada agajin gaggawa ta majalisar ɗinkin duniya ta ce a yanzu bata da zabin da ya wuce dakatar da aikinta saboda yanayin yadda yaƙin ya dauki zafi.
Ta cikin wata sanarwa da hukumar bada agajin gaggawar ta fitar, ta ce wannan mataki ba yana nufin ta dakatar da aikinta a yankin na din-din-din ba, sai dai yana nufin zata sararar don baiwa jami’anta kariya a dai-dai wannan lokaci mai matukar haɗari.
A baya dai hukumar ta mayar da kusan dukannin jami’anta zuwa yankin na Dier Al-Balah, bayan kutsen da Isra’ila ta yi a Rafah, amma kuma yanzu shi kansa wannan yankin ya fita daga sahun tundun mun tsira a Gaza.
- NNPCL ya fara fitar da iskar gas zuwa China da Japan
- Mai shayi ya kashe saurayi saboda taliyar yara a Jigawa
A Lahadin da ta gabata ne Isra’ila ta umarci dukannin fararen hular dake Deir Al-Balah da su fice daga yankin cikin wa’adin sa’o’’i 24-48 da ta basu.
A sanarwar da hukumar ta fitar ta ce babban ƙalubalenta shine samun waje mai tsaro da zata girke kayan aiki da kuma jami’anta ba tare da fargabar hari zai iya afka musu ba.
Wannan dai na zuwa ne a dai-ai lokacin da yaƙin ya laƙume rayukan mutanen da basu ji ba basu gani ba har dubu 40,435 a ƙarƙashin kiddidigar gwamnatin Hamas, yayin da majalisar ɗinkin duniya ta ce mafi yawa daga wannan adadi mata ne da ƙananan yara.