Majalisar Wakilai ta kammala karatu na farko a kan daftarin kasafin badi da Shugaban Muhammadu Buhari ya gabatar.
Majalisar ta kuma mika kasafin domin yi masa karatu na biyu a loakcin zamanta na ranar Laraba bayan ’ya’yanta sun kammala tofa albarkacin bakinsu a karatun farkon da aka fara a ranar Talata.
- Majalisa ta fara aiki kan kasafin 2021
- Atiku ya nemi Buhari ya janye kasafin kudin 2021 da ya gabatar
A jawabinsa kafin fara mahawara a kan kasafin, Shugaban Majalisar Wakilai, Femi Gbajabiamila ya bukaci hukumomin gwamnati su mika wa Majalisar rahoton aiwatar da kasafinsu na wata uku.
Gbajabiamila ya ce hakan zai taimaka wajen sanya hukumomin a mizanin da ya dace yayin nazarin tanade-tanaden kasafin.
Idan ba a manta ba a ranar Alhamis din makon jiya ne Shugaba Buhari ya gabatar da wa Babban Zauren Majalisar Tarayya daftarin kasafin na Naira tiriliyan 13.08.