Majalisar Dattawa ta tursasa kwamitinta mai lura da ayyukan sadarwa da ya aike goron gayyata zuwa ga Ministan Sadarwa, Isa Ali Pantami, domin jaddada masa bukatar aiwatar da kudurorin Majalisar game da inganta tsaro da ya shafi aikin ma’aikatarsa.
Kamar yadda doka ta 42 da 52 na kundin tsarin Majalisar ya tanada, bukatar hakan ta fito ne daga bakin Sanata Emmanuel Bwacha na jam’iyyar PDP mai wakiltar shiyyar Taraba ta Yamma.
- Shari’ar Batanci: An jibge jami’an tsaro a kotu
- Kungiyar ’yan jarida za ta karrama wasu fitattun ’yan Najeriya 7 a jihar Kano
Aminiya ta fahimci cewa Majalisar za ta aike da goron gayyatar ne domin kara fahimtar da Ministan bukatar amfani da ma’aikatarsa wajen dakile ta’addanci da kalubale na rashin tsaro a kasar.
Majalisar ta yanke shawarar hakan ne duba da yadda matsalar tsaro ke ci gaba da tabarbarewa a Najeriya musamman a yankin Arewa.
A cewar Sanata Bwacha, lamari na rashin tsaro ya wuce munzali na ci gaba da hauhawa domin kuwa ya kai mataki na intaha.
Ya ce kalubale na rashin tsaro ya bude kofar ta’addancin sata da garkuwa da mutane, fashi da makami, kashe-kashen mutane da sauran ababe na ta’ada a fadin kasar.
Sanatan ya kuma bayyana damuwa da yadda a kwanan baya aka yi wa Shugaban jam’iyyar APC na jihar Nasarawa kisan gilla da kuma wani dan kasar China da aka sace a jihar Taraba, lamarin da a cewarsa ba za su manta shi ba.
Ya kuma nuna damuwarsa kan zargin gazawa ta wasu jami’an gwamnati da aka dora wa nauyin tsare rayuka da dukiyoyin al’umma musamma idan aka yi la’akari a yadda ake samun wasu jami’an tsaro a ayyukan fashi da makami da garkuwa da mutane a sassan kasar.
Ya ce: “A Najeriya ne kadai za ka samu ana amfani da kayayyakin sadarwa kara zube ba tare da wata ingatacciyar hanya ta tantance ko da fasfo ne na bakin da suke shigo wa kasar.”
“A yanzu masu garkuwa da mutane da neman kudin fansa na amfani da kafofin sadarwa irinsu wayar salula wajen cin karensu babu babbaka da tumke damarar da suka kulla.”
“Ta ya za a yi ’yan ta’adda su rika tattauna wa da ’yan uwan wadanda suka yi garkuwa da su har su karbi kudin fansa ba tare da an yi amfani da wannan dama ta sadarwa ba wajen cafke su?”
“Irin wadannan miyagu suna samun nasara ne a sakamakon rashin kula da kuma mummunan yanayi na hanyoyin sadarwa a kasar da kuma gazawar jami’an tsaro da rashin ingancin ayyukan kamfanonin sadarwa.”