’Yan majalisar sun yi ca a kan kudurin dokar wadda ta bukaci a karfafi cibiyoyin ilimi mallakar gwamnati a Najeriya, daga barazanar da suke fuskanta daga na kasashen waje da suke ta yawaita a kasar.
- Zan fice da PDP zuwa NNPP kafin karshen wata —Kwankwaso
- Gwamnati ta sa a tura Abba Kyari Amurka ya fuskanci hukunci
A martaninsa ga kudurin dokar, Honorabul Leke Abejide, ya ce: “Shin ana nufin sai in cire ’ya’yana daga makarantun da suke a kasar waje ke nan, duk da cewa tun kafin in zama dan Majalsiar Wakilai suke karatu a can?”
Amma mai gabatar da kudirin, Honorabul Sergious Ogun, ya bukaci ’yan Majalisar su karanta kudurin dokar a natse su fahimci duk da ta kunsa, ba wai su tsaya a kan abu daya ba.
Honorabul Ogun ya bayyana cewa manufar dokar ita ce taka burki ga yadda jami’an gwamnati da masu rike da mukaman siyasa suke tura ’ya’yansu karatu a kasashen waje ba tare da sun yi abin da ya kamata ba wajen inganta makarantun gamnati ba na cikin gida
Daga karshe dai Majalisar ta yi watsi da kudurin a lokacin karatu na biyu a kansa da suka yi a zaman da Mataimakin Shugaban Malisar, Honorabul Ahmed Idris, ya jagoranta a ranar Alhamis.