✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Majalisa ta yi wa kudirin daure ’yan daudu karatun farko

Duk wanda aka kama yana aikata daudu ya yi laifin da zai fuskanci hukuncin cin sarka na wata shida.

Majalisar Wakilai ta yi wa kudirin da ke neman a soma daure ’yan daudu watanni shida a fadin Najeriya karatun farko.

Wannan na zuwa ne yayin gabatar da kudirin da ke son a yi wa Dokar Haramta Auren Jinsi kwaskwarima.

Da yake karanto sashe na 4 na dokar a ranar Talata, dan majalisa mai wakiltar Toro daga Jihar Bauchi, Umar Muda Lawal, ya nemi a haramta daudu a fili ko kuma a boye.

Ya nemi a saka daurin wata shida a cikin dokar ko kuma tarar naira 500,000 ga duk wanda aka kama a matsayin dan daudu.

Dan majalisar na so a kara wani karamin sashe na 4 cikin baka a cikin Dokar Haramta Auren Jinsi ta 2013 da zai ayyana cewa: “Duk wanda aka kama yana aikata daudu ya yi laifin da zai iya fuskantar hukuncin zaman gidan yari na wata shida ko kuma tarar N500,000.”

Bayan karatun farkon da aka yi kudirin daure ’yan daudun ko cin su tara a ranar Talata, zai zama doka idan ya sha karatu na biyu da na uku.