✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Majalisa ta yi barazanar soke kasafin hukumar wutar lantarki

Majalisar Wakilai ta yi ce za ta soke Naira biliyan biyu daga cikin kasafin 2021 na Hukumar Kula da Wutar Lantarki na Najeriya (NERC). Shugaban…

Majalisar Wakilai ta yi ce za ta soke Naira biliyan biyu daga cikin kasafin 2021 na Hukumar Kula da Wutar Lantarki na Najeriya (NERC).

Shugaban Kwamitin Wutar Lantarki na Majalisar, Magaji Da’u Aliyu ya fadi haka ne a lokacin da Shugaban NERC, James Momoh ya bayyana domin kare kasafin hukumar a ranar Laraba.

James Momoh ya shaida wa kwamitin cewa hukumarsa na bukatar Naira biliyan biyun ne don yin shamakin katako da kuma kujeru da tebura a ginin hedikwatar hukumar.

Ya bayyana wa ‘yan kwamitin cewa sanya shamakin da sayen kayan a sabon ginin hedikwatar hukumar na da matukar muhimmanci domin dacewa da yanayin aiki.

A cewarsa, an dade ana gudanar da aikin hedikwatar hukumar kuma an sanya kudaden a kasafin 2020 da 2021 na hukumar.

Sai dai ya ce NERC ba ta samu kashe dudaden da aka ware wa aikin ba a 2020 saboda annobar COVID-19.

Da jin haka, kwamitin ya bukaci hukumar ta gabatar da jawabin kudaden da aka kashe a kan ayyukan sanya shamaki da kujeru da aka rika aka kammala.

Shugaba Kwamitin ya ce majalisar za ta soke bukatar muddin ba hukumar ba ta gabatar da bayanan kudade da sauran ayyukan da aka rika aka kammala ba.