Majalisar Dattawa jiya ta amince da bukatar Shugaba Muhammadu Buhari na ciyo bashin dala biliyan biyar da digo biyar daga kasashen waje don daukar nauyin manyan ayyuka na kasafin kudin bana da kuma biyan bashin cikin gida.
Amincewar ta biyo bayan lamincewar da kwamitin majalisar kan basussukan ciki da waje wanda Sanata Shehu Sani daga na APC daga jihar Kaduna yake jagoranta.
An gabatar da bukatar Buharin a dandalin majalisar a ranar 10 ga watan Oktoban wannan shekarar nan inda daga cikin bashin dala biliyan biyu da rabi za a biya bashin kasashen waje wacce aka zartar da doka a kan haka a shekarar 2017 sauran Dala biliyan uku kuma za a biya basussukan cikin gida ne.