Majalisar Dattawa ta tabbatar da nadin Mista Shaakaa Chira a matsayin babban mai binciken kudi na tarayya.
Har ila yau, ta amince da nadin mutane bakwai a matsayin Kwamishinonin Hukumar Zabe ta Kasa INEC (RECs).
- Kotu ta yanke wa wanda ya watsa wa budurwarsa ruwan batir daurin rai da rai
- Wahalar takardun kudade ta fara dawowa a Kano da Borno
Wadanda aka amince da nadin nasu su ne Etekarnba Umoren (Akwa Ibom), Isah Shaka Ehimeakne (Edo), Oluwatoyin Babalolo (Ekiti), Abubakar Ahmed Ma’aji (Gombe), Shehu Wahab (Kwara), Aminu Kasimi Idris (Nasarawa), da Mohammed Abubakar Sadiq (Neja).
Ragowar ukun sun hada da Anugbum Onuoha daga Ribas, Abubakar Fawa Dambo daga Zamfara da Bunmi Omoseyindemi daga Legas.
An tabbatar da nadin wadanda aka zaba bayan an tantance su a zauren Majalisar Dattawa a ranar Laraba.
A wata wasikar Shugaba Bola Ahmed Tinubu da aka karanta a ranar Talata, ta bukaci majalisar ta tabbatar da wadanda ya nada.
A cikin wasikar, Tinubu ya ce bukatarsa ta tabbatar da wadanda ya zaba a majalisar ta yi daidai da tanadin tsarin kundin mulki.
Kwamishinonin da aka tabbatar za su yi wa’adin shekara biyar kowannensu.