✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Majalisa ta kayyade kudin da ‘yan takara za su kashe a yakin zabe

A ranar Talatar da ta gabata ce Majalisar Dattawa ta amince da wata doka da ta kayyade kudin da ’yan takara za su iya kashewa…

A ranar Talatar da ta gabata ce Majalisar Dattawa ta amince da wata doka da ta kayyade kudin da ’yan takara za su iya kashewa a lokacin yakin neman zabe a shekarar 2019.

Dokar ta hana ’yan takara kashe kudaden zabe da suka zarce kima, inda ta bukaci kada dan takarar Shugaban Kasa ya wuce Naira biliyan 5. Dan takarar Gwamna kuma kada ya wuce Naira biliyan 1, yayin da ’yan takarar Majalisar Dattawa kada su wuce Naira miliyan 250.

Dokar ta ce ’yan takarar Majalisar Wakilai kada su wuce Naira miliyan 100. Dokar zaben kuma ta bayyana yadda za a yi amfani da na’urar zabe a lokacin tantance masu kada kuri’a a rumfunan zabe.

Masana kan harkokin zabe sun  ce wannan matakin zai rage yawan yadda ake amfani da kudi wajen gudanar da zabe a kasar nan.

An yi amfani da na’urorin tantance masu kada kuri’a a zaben 2015, amma an rika samun korafe-korafe kan cewa ba sa aiki a wasu lokutan, musamman ma a yankunan da ake fama da rashin wutar lantarki.

A karkashin wannan doka da majalisar ta kafa, ya zama wajibi a yi amfani da na’urar tantance masu kada kuri’a, amma idan aka samu tangarda kuma ba a iya maye gurbinta da wata ba cikin sa’a uku, to za soke zaben da aka gudanar a wannan akwati, kana a sake gudanar da wani sabon zaben cikin sa’o’i 24.