Majalisar kasa jiya ta amince da tsarin kashe kudi na MTEF na shekarar 2018 zuwa shekarar 2020 inda ta kara farashin mai daga Dala 45 zuwa Dala 47 a kowace ganga.
Tuni kasafin kudin da shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar ga majalisar na shekarar 2018 a watan Nuwamban shekarar da ya gabata ya haye karatu na biyu.