Majalisar Dattawa ta kafa kwamiti mai mambobi 45 da za su yi aikin gyaran fuska ga kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999.
Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ne ya sanar da kafa kwamitin a ranar Laraba, yana mai cewa za a kaddamar mambobin a ranar Talatar makon gobe kuma nan take za su fara aikin.
Akpabio bayyana cewa kundin tsarin mulki na 1999 yana bukatar sake dubawa, saboda a cikinsa akwai batutuwa da dama da ya kamata a gyara su.
Ya ce kwamitin yana da wakilcin sanata daya daga kowace jiha da kuma Abuja, sai kuma wakili daya daga kowace shiyyar siyasar kasar nan.
- Rashin Tsaro da Yunwa: Mun San Mafita Aiwatarwa Ne Matsala —Sarkin Musulmi
- Makiyaya sun kona gidaje 146, mutane 1,600 sun tsere a kauyukan Yobe
Sanata Akpabio ya bukaci a gabatar da duk shawarwari da bangororin kundin tsarin mulkin kasar da ake bukatar su yi wa kwaskwarima wa kwamitin.
Shugaban majalisar ya kuma umarci kwamitin ya gayyaci shugaban majalisar dokokin kowace jiha domin tattaunawa da ba da gudummawarsu.