✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Majalisa ta hana kashe N10bn kan sayo rigakafin COVID-19

Ta taka wa Ministan Lafiya burki kan kashe kudaden da aka bayar

Majalisar Tarayya ta hana Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya kashe Naira bilyan 10 kan rigakafin cutar COVID-19 a Najeriya.

Kwamitin Lafiya na Majalisar Dattawa ya ce umarci Ma’aikatar ta dakatar da kashe kudaden da Gwamnatin Tarayya ta fitar wajen samar da rigakafin cutar.

Shugaban Kwamitin, Sanata Ibrahim Oloriegbe ya ce Naira biliyan 10 din ba an ware su ne domin sayen rigafin COVID-19 ba, sannan sauran bangarorin da abin ya shafa ba su cika ka’idojin yarjejeniyar ba.

A makon jiya ne Ministan Lafiya, Osagie Ohanire, ya sanar cewa an ba su Naira biliyan 10 domin taimaka wa samar da rigakafin COVID-19 a cikin gida.

Ministan ya bayyana hakan ne a lokacin taron jawabin kwamitin yaki da cutar da Shugaban Kasa ya kafa.

Kwamitin Majalisar ya bukaci Ministan da ya gabatar masa da takardun da suka dace da kuma yarjejeniyar da aka kulla tsakanin gwamnati da kamfanoni.