✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Majalisa ta dakatar da Shugaban Karamar Hukumar Nasarawa

Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa ta dakatar da Shugaban Karamar Hukumar Nasarawa, Mohammed Sani Ottos bisa laifin rashin biyayya. Ta kuma dakatar da Mataimakin Shugaban Karamar…

Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa ta dakatar da Shugaban Karamar Hukumar Nasarawa, Mohammed Sani Ottos bisa laifin rashin biyayya.

Ta kuma dakatar da Mataimakin Shugaban Karamar Hukumar Karu, Lawal Yakubu Karshi bisa laifin rashin biyayya.

Shugaban Majalisar, Ibrahim Balarabe Abdullahi ya yanke hukuncin bayan Shugaban Kwamitin Kananan Hukumomi a Majalisar, Barista Mohammed Alkali ya gabatar da kudirin dakatar da su a zaman gaggawan da majalisar ta yi.

Ya ce barin aikin gwamnati da wadanda aka dakatar din suka yi domin zuwa sauraron shari’ar tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar, Aliyu Tijani Ahmed, cin mutuncin aiki ne da rashin da’a.

“Saboda haka an takatar da Shugaban Karamar Hukumar Nasarawa har sai an kammala bincike. Daga yanzu, an umarci Mataimakin Shugaban Karamar Hukumar Nasarawa da ya ci gaba da jan ragamar mulki”, inji Shugaban Majalisar.

Ya kuma umarci Kwamishinan ‘Yan Sanda da ya sama wa Mukaddashin Shugaban Karamar Hukumar tsaro na tsawon lokacin da za a gama binciken.

Abdullahi ya kuma nuna takaicin yadda Shugaban Karamar Hukumar ya yi watsi da mutanensa a jaribirin zabe don halartar zaman kotun da bai shafe shi ba maimakon ya tsaya ya taimaka wa jami’an tsaro a tabbatar zaben maye gurbin Nasarawa ta tsakiya cikin lumana.

Ya kuma ce, Shugaban karamar hukumar ya fi yi wa tsohon Sakataren Gwamnatin biyayya fiye da mulkin da aka zabe shi ya gudanar.

Honarabul Mohammed Alkali ya gabatar da kudirin dakatar da Shugaban karamar hukumar, sai Honarabul Daniel Ogazi ya aminta da shi.

Shugaban Majalisar ya kuma nada kwamitin mutum bakwai su binciki abun da ya faru a kananan hukumomin biyu. Ya kuma basu watanni uku su gabatar masa da rahoto.