✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Majalisar Dattawa ta tsige Sanata Ali Ndume

Ganduje ya bukaci Sanata Ndume ya fice daga APC ya koma duk jam'iyyar adawa da yake sha'awa

Majalisar Dattawa ta tsige Sanata Ndume daga kujerarsa ta mai tsawatarwanta.

Sauke Ali Ndume daga kujerar na da nasaba da zargin Gwamnatin Shugaba Tinubu da rashin daukar mataki wajen magace yunwa da ke addabar al’ummar Najeriya.

Ndume wanda shi ma dan Jam’iar APC mai mulki ne ya kuma yi zargin cewa Shugaba  Kasa Bola Tinubu bai san halin da al’umma ke ciki ba, kuma akwai wadanda suke hana shi ganin jama’a da yin magana a kan al’amara.

A zaman ranar Larba shugaban majalisar, Godswill Akpabio, ya gabatar da kudurin tsige Ndume, wanda kuma yan Jam’iyyar APC suka goyi baya.

A halin da ake ciki majalisar ta maye gurbin Ndume da Sanata Tahir Mungono (Borno ta Arewa) a matsain sabon mai tsawatarwa.

Wata wasika da uwar Jam’iyyar APC ta aike wa mambobinta a majalisar ta bukaci Sanata Ndume ya fice daga cikinta ya koma duk jam’iyyar adawa da yake sha’awa.

Wasikar na dauke da sa hannun Shugaban APC na Kasa Abdullahi Ganduje, da Sakatare, Barista Ajibola Bashiru.

Majiyoyi a Majalisar sun bayyana cewa baya ga tsige Sanata Ali Ndume, magoyon bayan Tinubu na kokarin gani an dakatar da shi.

Wannan na zuwa ne watanni bayan majalisar ta dakatar da Sanata Abdul Ingila na watanni uku, saboda ya yi zargin cushen Naira tiriliyan 3.7 a kasafin kudin 2024, a yayin hirarsa da Sashen Hausa na BBC.

A lokacin wata hira da ’yan jarida a Majalisar Dattawa a makon jiya ne Ndume ya yi zargin cewa, Tinubu “ba shi da masaniya kan abubuwan da ke faruwa a wajen Fadar Shugaban Kasa.

“Wasu sun tare shi, yawancinmu kuma ba za mu iya bi ta bayan fage ba ballantana mu samu ganin shi.

“Yanzu sun ma hana shi yin magana a kan abubuwa, sannan ba shi da masu ba shi shawara kan al’amuran al’umma, sai kakakinsa, Ajuri Ngelale, da ke rubuta masa jawabi.

“’Yan Najeriya sun fusata; Gwamnati ba ta yin komai kan matsalar yunwa, wanda muka ke buƙatar a gaggauta daukar mataki.

“Ba mu da abinci a ajiye, akwai ƙarancin abinci, rashin abinci ne matsala mafi muni da za ta iya samun wata ƙasa.

“Karin munin lamarin shi ne haduwar wannan matsalar da ta tsaro.”

Wadannan kalaman ne suka ja wa Ndume suka daga wasu sanatocin jam’iyyarsa ta APC magoya bayan Tinubu.

Kan gaba a cacckar Ndume shi ne Sanata Sunday Karimi (Kogi West) da kuma APC.