Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa ta dakatar da Babban Hadimin Gwamnan Jihar kan Cigaban Kasa, Stanley Buba saboda zargin almundahana a Hukumar Raya Birane ta Jihar (NUDB).
Shugaban Majalisar, Ibrahim Balarabe Abdullahi ya sanar, bayan hadimin gwamnan ya amsa tambayoyi a zauren majalisar kan zargin da ake wa ofishinsa, cewa akwai bukatar Stanley ya koma gefe domin a gudanar da cikakken bincike kan NUDB ba tare da cikas ba.
“Zauren Majalisar ya amince Babban Hadimin Gwamna Abdullahi Sule kan Cigaba, Stanley Buba ya koma gefe a gudanar da cikakken bincike”.
‘Yan Majalisar sun nemin sanin mai kula da kudaden NUDB, da mai sanya hannu a fitar da su a kwamitin daraktocin hukumar, wanda Buba ya shaida musu cewa Manajan Darekna hukumar ne.
Ya kara da cewa ayyukan da gwamnan ya ba shi sun hada da bayar da izinin fitar da kudade.
Shugaban Majalisar ya ce an gayyaci Buba ya yi bayani kan dalilinsa na yin zagon kasa ga umarnin Malisar kan rikicin shugabancin kwamitin daraktocin NUDB.
A ranar 1 ga Satumba, 2020 majalisar ta yanke hukuncin sasanta rikicin shugabancin hukumar tsakanin Manajin Darakta Adamu Sule da kuma Stanley Buha.
Kwamitin Majalisar ya ce dokar NUDB ta fayyace cewa Manajan Darektan hukumar shi ne Sugaban Kwamitin Darektoci.
“Domin a zauna lafiya, hadimin ya kula da ayyukan kwamitin daraktocin a yankin Yammaci musamman ofishin shiyya da ke Jos, amma izinin fitar da kudade zai kasance a hannun Manajan Darakta”, inji Majalisar, a wancan lokaci.
Kwamitin zai gabatar wa majalisar rahotonsa bayan wata uku.