✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Majalisa ta dage dawowarta daga hutu saboda taron APC

Majalisar za ta ci gaba da zamanta daga ranar Talata 14 ga watan Yuni, 2022

Majalisar Dokoki ta Najeriya ta dage ranar da ta sanya na dawowa daga hutun da ta tafi zuwa ranar 14 ga watan Yuni da muke ciki.

Majalisar ta daga dawowa da zaman nata ne saboda babban taro da zaben dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar APC.

Da farko Majalisar ta sanar da ranar Talata 7 gwa watan Yuni da muke ciki domin dawowa da zama, amma ta dage saboda tsaikon da aka samu bayan dage babban taron na APC.

Akawun Majalisar Wakilai, Yahaya Danzaria ya ce,  “Zaurukan Majalisar sun dage dawowarsu da zama daga ranar Talata 7 zuwa Talata, 14th ga watan Yuni, 2022 saboda babban taron jam’iyyar APC.