✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Majalisa ta bukaci a sanya gyaran ofisoshin ’yan sanda a kasafin 2023

Majalisar Wakilai ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta ware wani kaso na kasafin 2023 domin gyara ofisoshin ’yan sandan da suka lalace.

Majalisar Wakilai ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta ware wani kaso na kasafin 2023 domin gyara ofisoshin ’yan sandan da suka lalace.

Kiran dai ya biyo bayan gyaran fuskar da Majalisar ta yi ne ga kudirin da dan Majalisar Wakilai daga Jihar Bauchi, Mansur Manu Soro, ya gabatar a zaman Majalisar a ranar Laraba.

A kudirin nasa, Soro ya yi kira ga gwamnati da ta gyara ofisoshin ’yan sanda da na Sibil Difens da ke Mazabar Darazo/Ganjuwa a Jihar Bauchi.

Soro ya koka kan yadda Rundunar ’Yan Sandan Najeriya ke nuna halin ko-in-kula da gyaran ofishin ’yan sandan da ke garin Soro, wanda a halin yanzu ya daina aiki tun bayan harin da Boko Haram ta kai a 2013.

Ya kara da cewa shi aikin gina ofishin ’yan sanda na kananan hukumomin Sade da Darazo tuni gwamnati ta yi watsi da shi tun a 2017.

Sannan ya bayyana damuwa kan halin dari-darin da jami’an tsaron Sibil Difens suke aiki aciki a garin Darazo, saboda karancin ofisoshinsu da na ’yan sanda.

Da yake tsokaci a kan kudirin, dan majalisa Ifeanyi Chudi Momah daga Jihar Anambra ya bukaci a hada da ofishin ’yan sanda na Ihiala, kuma Majalisar ta amince.

A karshe Majalisar ta umarci Asusun Tallafa wa Rundunar ’Yan Sanda da ta gyara caji ofis din da ke Soron, ta kuma zuba musu kayan aiki.

Majalisar ta kuma ba wa Hukumar Sibili Difens ta Kasa da kuma Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida umarnin su yi garambawul ga ofisoshin Sibil Difens da ke aiki a garuruwan Darazo da Ihiala.

Kazalika ta ba wa hukumomi da sauran masu ruwa da tsaki wa’adin sati takwas domin kawo mata rahoto kan kudirin domin daukar mataki na gaba.

Ta kuma yi kira ga gwamnati da ta ware wani kaso na kudi a kasafinta na 2023, domin gyaran baki dayan ofisoshin ’yan sandan kasar nan.