Zaman Majalisar na ranar Talata ya bukaci Gwamnatin Tarayya ta sauya sunan filin jirgin domin tunawa da Ajimobi wanda shi ne Mataimakin Shugaban Marasa Rinjayenta a shekarar 2003 zuwa 2007, a lokacin da ya wakilci mazabar Oyo ta Kudu.

Mika bukatar hakan ga gwamnatin tarayya ta biyo bayan kudurin da Sanata Abdulfatahi Buhari (APC, Oyo) ya gabatar a lokacin zaman majalisar, wadda ta samu goyon bayan takwarorinsa.

Zauren majalisar ya kuma yi shiru na minti daya domin juyayin rasuwar tsohon gawmnan na Oyo wanda ya rasu a narar 25 ga watan Yuni yana da shekara 70 a duniya sakamakon rashin lafiya.