✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Majalisa ta ba NNPC mako daya ya kawo karshen wahalar mai a Najeriya

Majalisar ta ce ba ta bukatar karin kirfi daga NNPC

Majalisar Wakilai ta umarci Kamfanin Mai na Najeriya (NNPCL) da ya gaggauta kawo karshen wahalar man fetur din da ta ki ci, ta ki cinyewa a kasar nan cikin mako daya.

Umarnin ya biyo bayan wani kudurin gaggawa da dan majalisa Sa’idu Musa Abdullahi (APC, Neja) ya gabatar a zauren majalisar ranar Talata.

Da yake gabatar da kudurin, dan majalisar ya ce ’yan Najeriya a tsawon watannin da suka gabata sun jima suna fama da matsalar man wacce take yin mummunar illa ga tattalin arziki.

Ya ce Hukumar Kula Man Fetur ta Najeriya (NMDPRA) ta sha kawo dalilai marasa tushe kan abin da ya haddasa wahalar.

Dan majalisar ya ce, “Lokacin da matsalar ta fara ta’azzara a watan Oktoba a Abuja da sauran jihohin Arewacin Najeriya, sai NMDPRA ta bayar da hanzarin cewa ruwan saman da ya shanye gadar Lokoja ne ya gurgunta harkar sufurin man ya kuma kawo wahalar man.

“Amma lokacin da matsalar ta ci gaba, bayan duk dalilan da suka bayar sun kauce, sai kungiyar dillalai ta IPMAN ta ce rashin samun wadataccen man ne ya kawo wahalar shi.

“Sai dai bayanan sirri da jami’an tsaronmu suka tattara sun nuna cewa wasu dillalan suke boye man don yi wa gwamnati zagon kasa, sannan su kirkiri wahalar da ba ta Allah da Annabi ba ce.”

Ya yi koken cewa galibin gidajen mai a Najeriya yanzu sun koma sayar da man a kan sama da N300 kan kowacce lita.

Daga nan ne majalisar ta umarci NNPCL ya kawo karshen matsalar wahalar da ’yan Najeriya ke ciki, tare da umartar kwamitinta na harkokin man fetur da ’yan sanda da jami’an DSS su tabbatar ana sayar da man a kan farashin gwamnati.

Idan za a iya tunawa, ko a karshe makon da ya gabata sai da Hukumar Tsaron Farin Kaya (DSS) ta ba gidajen mai wa’adin sa’o’i 48 su kawo karshen matsalar.

Sai dai binciken Aminiya ya nuna har bayan karewar wa’adin har yanzu akwai sauran rina a kaba na matsalar, sai ma karuwar farashin da ake samu.