✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Majalisa ta ba da umarnin bincike kan kisan Kwamishinan Katsina

Majalisar dai ta bukaci a gano wanda suka kashe Kwamishinan.

Majalisar Tarayya a ranar Laraba ta ba Rundunar ’Yan Sandan Najeriya umarnin bincike tare da gano wanda suka yi wa kwamishina a Jihar Katsina, Dokta Rabe Nasir kisan gilla.

Umarnin ya biyo bayan kudirin da dan majalisa, Isansi Sallsu Iro, ya gabatar kan bukatar bincike a kan lamarin.

Ya bayyana yadda aka yi wa kwamishinan kisan gilla a gidansa da ke cikin birnin Katsina, a ranar 2 ga watan Disamba 2021.

Iro ya bayyana damuwa kan yadda matsalar tsaro ke ci gaba da ta’azzara musamman a yankin Arewa da ma kasar nan baki daya.

Ya ce kisan abin takaici ne, wanda ya ce ya jefa al’ummar Katsina cikin kaduwa da dimuwa.

Dan majalisar ya ce akwai bukatar jami’an tsaro su gudanar da bincike don gano wanda suka kashe Kwamishinan tare da gurfanar da su gaban shari’a.