Majalisar Dattawa ta Najeriya ta amince da bukatar Shugaba Muhammadu Buhari ta karbo sabon bashin Naira biliyan 850.
Shugaban kasar ya gabatar da bukatar karbo bashin ne, wanda ya ce za a yi amfani da shi don gudanar da wasu aikace-aikace a kasafin kudi na shekarar 2020, a wani sako da shugaban majalisar, Ahmad Lawan, ya karanta a zamanta na ranar Talata.
Bayan karanta takardar, Sanata Ahmad Lawan ya bukaci Kwamitin Majalisa Mai Kula da Al’amuran Kudi ya yi aiki da Ministar Kudi Zainab Ahmed don samo karin bayani a kan ayyukan da za a gudanar.
Amma daga bisani, shugaban Kwamitin Yada Labarai na Majalisar Dattawa, Sanata Ajibola Basiru, ya fitar da wata sanarwa da ke cewa majalisar ta amince a karbo bashin a cikin gida.
Da ma dai a sakonsa Shugaba Buhari ya bukaci majalisar ta bai wa gwamnati damar tattaro bashin ne a cikin gida.
Ya ce saboda halin da annobar coronavirus ta jefa tattalin arzikin duniya da kuma faduwar farashin mai ba zai yi kyau ba a karbo rancen daga waje.