Majalisar Dattawa ta amince da bukatar Shugaban Kasa Bola Tinubu ta nada masu ba shi shawara na musamman guda 20.
Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan ne ya karanta wasikar Tinubu a zauren majalisar a ranar Talata.
- Majalisar Wakilai: Gwamnonin APC sun goyi bayan takarar Abbas
- Kasashen da suka rage a Gasar Kofin Duniya ta ’yan kasa da shekaru 20
Sai dai a cikin wasikar da aka aike wa Majalisar Dattawan, shugaban kasar bai bayyana sunayen masu ba da shawara na musamman guda 20 ba da zai nada ba.
Amma bayan karanta wasikar, babban zauren majalisar ya amince da bukatar cikin gaggawa.