✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Majalisar Wakilai: Gwamnonin APC sun goyi bayan takarar Abbas

Gwamnonin APC sun kudiri niyar marawa takarar Abbas baya.

Shugaban Kungiyar Gwamnonin APC, Hope Uzodinma, ya ce kungiyar na goyon bayan Honorabul Tajudeen Abbas a takarar Shugaban Majalisar Wakilai.

A wata sanarwa da kwamitin yakin zaben Abbas ta fitar a ranar Litinin, Mista Uzodinma ya ce gwamnonin sun kuduri aniyar mara wa Benjamin Kalu (APC-Abia) baya a matsayin Mataimakin Shugaban Majalisar.

A cewar sanarwar, Mista Uzodinma ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karbi bakuncin tawagar yakin neman zaben Abbas da Kalu, inda ya ce jam’iyyar ta yi zabi mai kyau na mutanen da za su jagoranci majalisar.

Gwamnan ya yaba wa ’yan kungiyar da suka fito daga jam’iyyu takwas da suka samu kujeru a majalisar wakilai ta 10.

“Ina sake taya ku murnar nasarar da kuka samu a zaben da ya gabata, kuma ina yaba muku kan haduwar ku don kulla kawancen don neman takarar shugaban majalisar.

“Kun yi abin da ya dace don tallafa wa wadannan mutane biyu. Abin da muke yi a yau shi ne dimokuradiyya kuma APC ita ce jam’iyya mai mulki kuma a yanzu kuna da alhakin taimaka wa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta yi nasara.

“Dukkanmu mun san cewa bangaren gwamnati da ya fi daukar hankali shi ne majalisa kuma idan muka yi wasa da ita, zai shafi komai.”

Tun da farko Mista Abbas wanda shi ne dan takarar APC ya yaba wa kungiyar bisa goyon bayan da suka ba shi.

Ya nanata aniyarsa ta ganin an kafa majalisa ta 10 da za ta yi aiki wajen aiwatar da shirye-shirye da manufofin gwamnati.

A nasa bangaren, Kalu ya ce takararsa ta shafi yankin Kudu maso Gabas ne baki daya.

Ya ce an san yankin na cikin sabbin shugabannin da aka dora wa alhakin samar da sauyi mai kyau ga rayuwar ‘yan Najeriya.

A ranar 8 ga watan Mayu, uwar jam’iyyar APC ta ba da mukaman Shugaban Majalisar Dattawa ta 10 zuwa Kudu Maso Kudu da kuma Shugaban Majalisar Wakilai zuwa Arewa Maso Yamma.

Haka kuma ta amince da a nada tsohon gwamnan Akwa Ibom Godswill Akpabio a matsayin Shugaban Majalisar Dattawa, da kuma Abass daga Jihar Kaduna a matsayin shugaban majalisar wakilai.