✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Majalisa ta amince da kasafin 2021

An ware wa ayyukan yau da kullum tiriliyan N5.6, manyan ayyuka kuma tiriliyan N4.1

Majalisar Dattawa ta amince da kasafin kudin shekarar 2021 na Naira tiriliyan 13.5 da Shugaba Buhari ya gabatar mata.

A ranar Litinin Majalisar ta amince da kasafin wanda ta kara yawansa da Naira biliyan 5.05 daga biliyan 13.08 da ya gabatara watan Oktoba.

Zaman Majalisar ya amince da kasafin tiritayan N5.6 domin ayyukan yau da kullum; tiriliyan N4.1 don manyan ayyuka da kuma tiriliyan N3.3 domin biyan basuka.

Kasafin na 2021 ya kuma ware tiriliyan N4.1 domin asusun raya manyan ayyuka da kuma biliyan N495 domin hukumomin gwamnati.

Zauren ya amince da kasafin ne bayan sauraron rahoton Kwamitinsa na Kasafi, karkashin Sanata Barau Jibrin.