✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Majalisa ta amince da ƙudirin yi wa Alƙalai ƙarin albashi

Alƙalan Kotun Ƙoli za su samu albashin naira 4.2 duk wata.

Majalisar Wakilai ta amince da ƙudirin dokar ƙara wa alƙalan Najeriya albashi da alawus na wata-wata.

Aminiya ta ruwaito cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ne ya miƙa wa Majalisar ƙudirin dokar domin tantancewa tare da amincewa da shi a ranar Talata.

Ƙudirin da Majalisar Wakilan ta amince da shi a ranar Laraba ya bayar da albashin jimillar naira miliyan 5.3 a kowane wata ga alƙalin alƙalai na Najeriya (CJN).

Ƙudirin ya kuma ce sauran alƙalan Kotun Ƙoli za su samu albashin naira 4.2 yayin da Shugaban Kotun ɗaukaka ƙara zai riƙa ɗaukar albashin naira miliyan 4.4 duk wata.

Haka kuma, alƙalan kotun ɗaukaka ƙara za su riƙa karɓar albashin naira miliyan 3.7 duk wata, yayin da ƙaramin alƙali zai karɓi albashin naira miliyan 3.5 duk wata.

A cewar ƙudirin, albashin na wata-wata ya ƙunshi cikakken albashinsu ne da duk wani alawus-alawus na yau da kullum da suka haɗa da samar da mai da kuma kula da ababen hawa da dai sauransu.