✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Majalisa na neman a daina ba ’yan kasa da shekaru 16 gurabe a jami’o’i

Majalisar ta ce shekarunsu ba su kai gane abubuwa ba.

Kwamitin Ilimi na Majalisar Dattijai a ranar Talata ya ce zai bukaci yin kwaskwarima a dokar da ta kafa Hukumar Samar da Guraben Karatu a Manyan Makarantu ta Kasa (JAMB) ta yadda za a hana ’yan kasa da shekara 16 samun guraben karatu a jami’o’i.

A cewar kwamitin, bai kamata a kyale dalibai masu kasa da wadannan shekarun su sami guraben karatu a jami’o’i ba, la’akari da kurciyarsu wajen gane abubuwan da za a koya musu.

Mataimakin shugaban kwamitin, Sanata Akon Eyakenyi wanda ya bayyana hakan yayin ziyarar sa idon kwamitin zuwa shalkwatar JAMB ranar Litinin, ya ce sun gano wasu muhimman bangarori guda biyu da suke bukatar kwaskwarima a hukumar domin a inganta ta.

Sanatan wanda ya jaddada muhimmancin ilimi ga makomar Najeriya ya ce bangaren na bukatar cikakkiyar kulawa domin a farfado da shi.

Ya kuma bayyana JAMB a matsayin wata gada tsakanin makarantun sakandare da na gaba da su, yana mai cewa suna da muhimmiyar rawa wajen inganta ilimin kasar.

“Idan ba a karantar da daliban sakandare yadda ya kamata ba kafin a tura su zuwa jami’a, to alal hakika za a fuskanci matsala,” inji shi.

Sanata Eyakenyi ya kuma jinjina wa hukumar da shugabanta, Farfesa Ishaq Oloyede kan yadda ta gudanar da jarrabawar UTME ta bana.