Majalisar Tarayya ta fara bincike kan sama da fadi na Naira biliyan 7.5 mallakin Hukumar Kula da Tashoshin Jiragen Ruwa (NPA).
Majalisar Wakilai ta gayyaci shugabannin NPA su gurfana a gabanta domin bayani kan kwangilar aikin gabar ruwa da ta bayar a jihar Bayelsa a shekarar 2012.
Binciken Kwamitin Kudaden Gwamnati na Majalisar ya taso ne bayan Ofishin Babban Mai Binciken Kudi na Tarayya ya yi zargin saba ka’ida a bayar da aikin da kuma biyan ‘yan kwangilar.
Ofishin ya kuma yi zargin biyan ‘yan kwangilar kudaden motoci da aka sa su sayo amma ba su kawo ba.
Akwai kuma ayar tambaya a kan biyan su miliyan N344 fiye da kudaden ayyukan, amma suka yi watsi da ayyukan ba su kammala ba.
Manajan Darektan NPA Ahmed Rufa’i ya shaida wa Kwamitin cewa tun a shekarar 2012 Majalisar Zartarwa ta Tarayya ta amince da aikin.