Wani magidanci ya bukaci Kotun Shari’ar Musulunci a Kaduna ta umarci matarsa ta biya shi N320,000 a madadin aurenta.
Lauyan mijin matar, Safiyanu Saleh, ya ce duk da dai wanda yake karewa yana kaunar matarsa, amma ba zai hana ta neman ‘Khul’i’ ba.
- Faso ya sace kansa ya karbi kudin fansa daga mabiyansa
- DAGA LARABA: Dalilin Da Maza Ke Tsoron Auren Mata ’Yan Boko
“Na biya sadakin N70,000, amma ina bukatar ta kara mini N250,000 don ba ni damar yin wani aure,” in ji magidancin.
Tun da farko, matar ta bakin lauyanta, Abubakar Sulaiman, ta bukaci kotun ta warware aurensu da magidanta ta hanyar ‘Khul’i’.
Lauyan ya ce matar ba ta da bukatar ci gaba da zaman auren, kuma a shirye take ta maida wa maigidan nata N70,000 da ya biya a matsayin sadakinta.
A cewar lauyan, “A dokar Musulunci, mace na iya neman rabuwa da mijinta ta hanyar mayar masa sadakin da ya biya ta, fiye ko abin da bai ka haka ba.
“Don haka muna rokon kotu ta bari mu biya kasa da haka saboda matsin tattalin arziki da ake fuskanta.
“Ko kuma a bar ta ta yi iddar wata uku a madadin biyan N70,000,” in ji shi.
Alkalin kotun, Malam Rilwanu Kyaudai ya dage shari’ar zuwa 24 ga Janairun 2023 don sasanta bangarorin biyu da kuma yanke hukunci.
Idda na nufin zaman da mace kan yi sakamakon rasuwar mijinta ko mutuwar aurenta, kafin ta iya sake yin wani auren.
(NAN)