Da safiyar yau Juma’a ne aka sanar da rasuwar maidakin Sarkin Daura Hajiya Binta Lolo Umar Farouk.
Hajiya Binta ta rasu tana da shekara 70 ta kwashe shekara tara tana jinya. Kamar yadda Sarkin Labarai Usman Ibrahim ya shaidawa Aminiya,
Marigayiyar ta rasu ta bar ‘ya’ya shida, biyu maza, hudu mata.
Daga cikin mazan akwai Danburan Daura Hakimin Baure Alhaji Daha Muhammad Umar Farouk.
- A karo na farko ba a yi sallar Juma’a ba a Kano
- COVID-19 a Daura: Yadda aka yi musayar zafafan kalamai
Kamar yadda Aminiya ta samu rahoton, Hajiya Binta tayi fama da ciwon hawan jini, ciwon suga da kuma na kafafu.
Tuni dai aka yi jana’ izarta a makabartar Gabas, yayin da Malam Salisu Rabi’u ya jagorancin sallar gawar.